Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da harin Isra'ila a Qatar
Gwamnatin Najeriya ta bi sahun wasu takwarorinta na duniya wajen yin Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai Qatar a ranar Talata.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar, ta yi kira ga duka ƙasashen biyu su kai zuciya nesa.
Gwamnatin Najeriyar ta ce ta yi matuƙar damuwa da hare-haren da Isra'ilar ta kai wa jagororin Hamas a birnin Doha.
Sanarwar ta ce Najeriya na kan doron martaba ƴanci da alfarmar kowace ƙasa, ƙarƙashin tsarin dokokin duniya, musamman a abin da ya shafi amfani da ƙarfin soji a kan wata ƙasa.
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar ta ce babu abin da harin zai haifar illa ƙara dagula lamurra a yankin Gabas ta Tsakiya, tare da kawo tarnaƙi ga yarjejeniyar diplomasiyya da ake ƙoƙarin amfani da ita wajen kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Gwamnatin Najeriya ta kuma yaba wa Qatar kan ƙoƙarin da ta ce ta jima tana yi wajen ganin ta zama mai ƙoƙarin wanzar da sulhu a yankin Gabas ta Tsakiya.
Haka kuma sanarwar ta buƙaci ƙasashen Isra'ila da Qatar su kai zuciya nesa domin guje wa dagulewar lamurra a yankin.
Daga ƙarshe gwamnatin Najeriya ta jajanta wa iyalan waɗanda harin ya rutsa da su tare da jaddada ƙudurin gwamnatin ƙasar na goyon bayan hanyar sasanci da tattaunawa don kawo ingantaccen zaman lafiya a yankin.

Comments