LABARAN RANA
Ƙungiyar ƙwadago ta
Najeriya wato NLC ta ce akwai buƙatar gwamnatin Najeriya ta sake duba yiwuwar
ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikatan ƙasar, domin a cewarta, naira 70,000 ya
yi kaɗan a yanzu da tattalin arzikin ƙasar ya taɓarɓare.
A watan Yulin bara ne
dai shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rattaba hannu a sabuwar dokar ƙara mafi
ƙarancin albashi, inda ya ƙara ƙaramin albashi na ma'aikatan ƙasar daga naira
30,000 zuwa naira 70,000, duk da cewa wasu jihohin na biyan sama da haka.
Kamfanin dillancin
labarai na Najeriya ya ruwaito ƙungiyar na cewa hauhawar farashin kayayyakin
buƙata a ƙasar ne ya sa mafi ƙarancin albashin naira 70,000 ba ya isar
ma'aikacin ƙasar gudanar da abubuwan da suke buƙata na rayuwar yau da kullum,
kamar yadda muƙaddashin babban sakataren NLC, Mr Benson Upah ya shaida wa NAN a
ranar Lahadi a Abuja.
"Maganar gaskiya
naira 70,000 ya yi kaɗan a wannan yanayin na taɓarɓarewar arziki a Najeriya.
Ma'aikata na fuskantar ƙalubale sosai, kuma idan gwamnati ba ta ɗauki matakin
da ya dace ba, lallai ma'aikatan ƙasar za su shiga cikin damuwa sosai.
"Tuni mun fara
tattaunawa da gwamnatin tarayya game da wannnan matsalar, kuma muna fata za ta
yi abin da ya dace duba da irin yadda tattalin arzikin ƙasar yake ciki."

Comments