Hilda Baci ta kammala girka shinkafa buhu 200 a tukunya ɗaya
Shahararriyar mai dafa abinci Hilda Baci ta kammala dafa katafariyar tukunyar shinkafa ranar Asabar wadda take sa ran kafa tarihin zama mafi girma a duniya.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa Hilda ta girka buhu 200 a cikin tukunyar mai faɗi da tsawon mita shida, wadda ke cin lita 22,619 a cikin kimanin awa tara.
Tun da farko matashiyar mai shekara 28 ta so girka buhu 250 na shinkafa samfurin Basmati, amma sai ta rage zuwa 200 saboda nauyin ya yi wa tukunyar yawa.
Dubban magoya baya ne suka taru a otel ɗin Eko da ke birnin Legas domin gane wa idonsu wannan aiki da aka yi wa laƙabi da "Gino World Jollof Festival".
Rahoton NAN ya ce an raba wa fiye da mutum 30,000 abincin da aka dafa a mazubai, ta yadda har sai da wasu suka kawo kwanuka daga gida.
Yanzu matashiyar tana jiran mahukuntan Guinness World Record (GWR) domin tantance girkin da ta yi da kuma bayyana shi a matsayin shinkafa mafi yawa da wani mutum ya dafa a tukunya ɗaya a tarihi.

Comments